TAJADIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (1)
Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin kai. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin dukkan halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halittu, Manzon Allah, Annabi Muhammadu, da Alayensa da Sahabban shi, da duk wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka, sakamakon sauraren hira da labaru da matasa suke yi a yankin Arewa maso yammacin kasar nan, da rubuce-rubuce da na ke cin karo da su a zaurukkan musayar ra’ayi na kafofin sada zumunta, musamman a Facebook da WhatsApp, na fahimci cewar akwai babbar barazana mai matsalar gaske da ta ke fuskantar arewacin kasar nan, musamman kuma yankin arewa maso yamma.
Wannan barazana kuwa ita ce: akwai wasu daga cikin Hausawa da suke kan wani Addini da ba na Musulunci ba, da wasu da aka haifesu Musulmi daga cikin Hausawa, sai dai yanzu babu ruwansu da Addini sun komai mulhidai, da suka dauko kwangila daga kasashen turawa da yahudawa, mai manufar haifar da mummunan tashin hankali da babban rikicin kabilanci tsakanin wadanda suke asalinsu Hausawa ne, da wadanda suke asalinsu Fulani ne , mazauna cikin garuruwa da birane, wadanda sun riga sun zama abu daya. Suna kokarin yin haka ne ta hanyar rusa Tajdidin Shehu Usman Dan Fodiyo, da ma Addinin Musulunci shi kansa, wanda shine ya zama silar kulla dankon zumunci mai karfi tsakanin mafi yawan kabilun Afrika ta yamma, kafin aure da haihuwa su kara kulla wannan zumunci.
Irin wadannan mutane sun riga sun ci nasara wurin zuga Fulanin daji cewar dukkan mazauna gari Hausawa ne manoma, koda kuwa asalinsu fulani ne, kuma abokan gabarsu ne. Sannan suka saukake masu hanyar samun makamai domin aikata ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso yamma. Suna kuma da hannu a cikin saukake wa ‘yan boko haram hanyar samun makamai domin tarwatsa Arewa maso gabas da sunan wani sabon yunkurin Addini wanda ba a bi ingantattun ka’idoji a cikin sa ba.
Babbar hanyar da suka dauko domin cimma manufofinsu a halin yanzu shine amfani da ta’addanci da yaran Fulanin daji su ke yi domin yada shubuhohi game da Tajdidin Shehu. Suna cewa Shehu shine ya fara jagorantar Fulani a cikin aikata ta’addanci da tawaye ga sarakunan kasar Hausa, ba domin yada Addini ba, sai don neman mulki da daukakar kabilar Fulani bisa ga ta Hausawa. Suna kira zuwa ga Hausawa da su yi wa sarakunan Fulani tawaye, su dawo da gidajen sarakunan Hausawa.
Irin wannan matsalar a yau ba ta takaita ne ba ga kasarmu kawai. Irin wadannan makiya musulunci da muka ambata suna nan suna aikin rura wutar kabilanci a kasashen Afrika ta Arewa: a Tunisiya da Moroko da Aljeriya da Libya suna gina kiyayyar Larabawa da yunkurin farfado da tarihi da al’adun kabilar Barbar. Haka a Misira ake ta faman sake farfado da rayuwar Fir’aunoni da kabilar kibdawa. Amma a karkashin duk wannan za ka ga cewa Addinin Musulunci ne dai ake kokarin rusawa ta hanyar tayar da rikicin kabilanci.
A wannan silsila ta wannan rubutu zan yi kokari in sha Allahu na kawo muna tarihin Tajdidin Shehu Dan Fodiyo a kasar Hausa, tare da kokarin warware kowace shubuha da makiyan Musulunci suke jefawa game da abubuwan da suka faru, ko wanne a muhallinsa in sha Allah.
Modibbon Gusau.
10/11/1446
H.
08/05/2025M.




