TAJDIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (4).
MANHAJAR TATTAUNAWA (2).
A . GABA TA FARKO, TAMBAYA TA FARKO (1):
Tambaya ta farko da zamu yi kokarin bayar da amsarta ita ce:
“Menene amfanin Tajdidin Shehu Dan Fodiyo ga kasar Hausa da Arewacin Najeriya a addinance da siyasance da abunda ya shafi yanayin zamantakewa da tattalin arziki?”
Amfanin Tajdidin Shehu a wannan nahiya ta duniya a wadannan fagage yana da yawa. Za mu daukesu da daya – daya in sha Allahu.
1 . A ADDINANCE:
Duk wanda ya ke Musulmi na kwarai mai kishin addininsa, ba mai fifita kishin wasu abubuwa ba a kan Addini, kamar kabilanci, zai yi murna da alfahari da irin ci gaban Addinin Musulunci da aka samu a wannan yanki namu sakamakon Tajdidin Shehu. Kadan daga cikin wannan ci gaba da aka samu ya hada da:
a . DABBAKA SHARI’AR MUSULUNCI CIKAKKIYA.
Ko Kilapaaton (Clapperton), wanda rubuce – rubucensa ne masu sukar Tajdidin Shehu da yunkurin kabilanci da neman mulki suka dogara, kamar su “Gimbiyar Hausa” da “Jarumar Hausa”, ya tabbatar a cikin dukkan rubuce – rubucen sa game da daular Musulunci da Shehu ya samar cewar an ginata bisa dabbaka cikakkiyar shari’ar musulunci bisa karantarwar Kitabu da Sunnah. To balle rubuce-rubucen da shi Shehun da kansa ya yi, da na dansa Muhammadu Bello da kanensa Abdullahi.
Musulunci ya shigo ne kasar Hausa a karni na 13 zuwa na 14 miladiyya. Su ma Fulani a daidai lokacin suka zo kasar Hausa da Barno suna musulminsu. Malaman Fulani sun taimaka kwarai wurin yada musulunci da karantar da shi a kasar Hausa.
An yi Sarakuna a kasar Hausa da Barno kafin Tajdidin Shehu wadanda suka dabbaka cikakkiyar shari’ar musulunci a masarautunsu, kamar Ali Gaji na Barno da Muhammadu Rumfa na Kano da Muhammadu Korau na Katsina. Amma sau da yawa idan irin wadannan Sarakunan suka wuce sai a maye gurbinsu da masu sha’awar duniya da zalunci da raya al’adun gargajiya.
Ko da Shehu ya fara wa’azi irin wadannan Sarakunan ya tarar a kasashen Hausa da Barno, kamar yadda Muhammadu Bello ya tabbatar wa Shehu Alkanemi a cikin wasikun da suka yi musaya, shi Alkanemin ya kasa kore cewar Sarakuna suna saka talakawa suna ayyukan shirka.
Shi ya sa babbar manufar Dan Fodiyo itace Tajdidin musulunci ta hanyar dabbaka cikakkiyar shari’ar musulunci, abunda kuma ya yi kenan.
Wannan daula ta musulunci mai aiki da tsuran shari’ar musulunci ba kuma ta takaita ga kasar Hausa ne kawai ba. Ta kunshi kasashen kabilu da yawa da a halin yanzu suke cikin Arewacin Najeriya , kamar mafi yawan kasar Barno ta da, da kasar Yarbawa da ta Nufawa da Gwari da Dakarawa da Gungawa da Kambarawa da sauransu. Ta hada da kasar Azbinawa da Zabarmawa da ke kasar Nijar a yau. Ta kuma shiga cikin kasar Chadi da Kamaru da Barkina Faso.
Ashe ka ga duk da cibiyar daular Shehu kasar Hausa ne amma ta wuce kasar Hausa. Daula ce ta Musulunci da ta shafi kabilu da yawa da kasashe da yawa.
Modibbon Gusau
16/11/1446
14/05/2025.




