Muhammad al-Bashir, sabon Firayim Ministan Syria, injiniya ne kuma ɗan siyasa wanda aka haifa a Jabal Zawiya a yankin Idlib na Syria a shekarar 1986. Ya samu digiri a fannin injiniyar lantarki da sadarwa daga Jami’ar Aleppo a 2007, sannan ya ci gaba da karatun shari’a da dokoki a Jami’ar Idlib inda ya kammala a 2021 tare da digiri mai daraja ta farko.
Al-Bashir ya kasance shugaban gwamnatin masu fafutukar ‘Salvation Government’ a arewacin Syria tun Janairun 2024 kafin a naɗa shi firayim minista. A baya, ya rike mukamin Ministan Ci Gaban Jama’a da Harkokin Jin Kai.
Sabon mulkinsa ya mayar da hankali kan ci gaban fasaha, gina tattalin arziki, da sauƙaƙa zaman lafiya a yankunan da yakin basasa ya shafa.
Mai Rahoto;
Mujahid Muhammad Tasiu.
At-tajdid News.




