Palasdinawa na fuskantar mummunar barazana ya yin da suke zuwa karbar kayan agaji kamar yadda Haaretz ya bayyanawa majiyar At-tajdid News cewa “Mun sami umarnin harbi kan Falasdinawa dake kusa da cibiyoyin agaji na Gaza” a cibiyoyin ba da agaji ba tare sun kawo barazana ko kuma daukar makami ba, an mayar da cibiyoyin ba da agajin tamkar fagen fama ta hanyar amfani da muggan makamai.
A wani harin bom da Isr@’ila ta kai kan wani tantin ‘yan gudun hijira a Mawasi, Khan Yunis ya yi sandiyar mutuwar mutane uku kamar yadda Cibiyar lafiya ta Nasser Medical Complex ta tabbatar.
‘Yan kama wuri zauna su kai mummunan hari da makamin roka a gabashi da arewacin Khan Yunis kamar yadda wakilin Aljazeera ya tabbatar.
Jami’an ba da agaji Al-Shifa sun shaidawa manema labarai mutuwar wani mai kamun kifi sakamakon gobarar da sojojin ruwan Isr@’ila suka sanya a gabar tekun Gaza.
Mai rahoto,
M.B.S.Gama.




