Mutum 7 Sun Mutu Sakamakon Hadarin Mota A Titin Zariya-Kano
Daga Hamza Lawan Kura
A kalla mutum bakwaine aka tabbatar da sun mutu sakamakon wani Hadarin mota da ya afku a garin ciromawa dake kan titin zariya zuwa Kano.
Hadarin ya faru ne sakamakon a jiya wata motar daukar kaya (Trailer) a gefen titi ba bisa kaida ba, wadda hakan ya Sanya wata Bus kirara Hummer ta shiga karkashinta.
Hummer an tabbatar da cewa ta taso ne daga garin Akwama na Jihar Benin zuwa kano lo kacin da hadarin ya afku, dukkanin wadan da suka rasu an tabbatar da fasunjojon wannan motar ne.
Da yake bayani wani wadda abin ya faru a gabansa ya shaidawa Majiyar Altajdid News cewa mutum daya ne ya tsira da ransa daga cikin mutum takwas dake cikin motar.
Bayan afkuwar Hadarin an kwashe wadanda abin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Kwanciya dake garin Kura, inda aka tabbatar da rasuwar dukkanin fasinjojin




