By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis
International News

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid
Last updated: 2025/11/10 at 2:20 PM
Attajdid Published November 10, 2025
Share
SHARE

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

 

Sojojin Isra’ila na ci gaba da rushe gidajen Falasɗinawa a unguwar Zeitoun da ke kudu maso gabashin birnin Gaza, yayin da suke kuma kai hare-hare ta sama masu ƙarfi kan birnin Khan Younis a kudu.

Sojojin mamaya na Isra’ila na ci gaba da rushe gidaje a unguwar Zeitoun, yayin da motocin soji ke luguden wuta sosai a gabashin birnin, kuma nau’uka daban-daban na jiragen sama marasa matuƙa na shawagi a yankin yammacin birnin.

Jiragen yaƙi na Isra’ila na kuma kai hare-haren sama masu tsanani a yankunan arewa da gabashin Khan Younis, yayin da aka harba makaman atilari na Isra’ila suka harba wasu bamabamai a yankin Zanna, da ke arewa maso gabashin birnin.

Yawancin rushe-rushen ana aiwatar da su ne a gaban wurin da aka shata “layin rawaya,” a cikin yankin da sojojin Isra’ila suka mamaye.

“Layin rawaya” na nufin yankin da sojojin Isra’ila suka janye zuwa gare shi bisa yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. Layi ne wanda ido bai iya gani wanda ya ratsa Gaza sannan ya raba yankin na Falasɗinawa gida biyu.

Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 241, yayin da wasu 619 suka jikkata, kuma an ciro gawawwaki 528.

Wannan ya sa jimillar adadin mutanen da suka mutu tun lokacin da Isra’ila ta fara yaƙin kisan kare dangi a Gaza a 7 ga Oktoban 2023 ya kai 69,176 sai kuma mutum 170,690 suka jikkata.

Mai rahoto;
M.B.S.Gama.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

TRUMP AND CHRISTIAN GENOCIDE IN NIGERIA

Attajdid November 10, 2025 November 10, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Gwamnatin Nijar ta Dakatar da Watsa Shirye-Shiryen BBC a ƙasar

Attajdid Attajdid December 13, 2024
Payment of NBAIS Examination Fees – NAPAIS Commends Kano State Government
Sakon Kungiyar Hamas ga Mutanan Duniya!!!
Hezbollah ta tabbatar da kisan shugabanta Hassan Nasralla
Ana Saran Za a Cimma Mastaya Akan Tsagaita Da Kuma Musayan Bursunonin Falasdinu da Isra’ila
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?