– Janar MusaBabbab Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce kwanakin ɗan bindiga, Bello Turji da sauran manyan ƴan bindiga da suka addabi ƙasar sun kusa ƙarewa a daidai lokacin da sojoji suke cigaba da aiki a jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma.
Ya ce kashe Kachalla Halilu Sububu, wanda ƙasurgumin ɗanbindiga ne ya cikin nasarorin da sojojin suke samu.Janar Christopher ya ƙara da cewa wani aikin soji na musamman mai suna “Fansar Yamma a Arewa maso Yamma,” da za a ƙaddamar ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.
Ya ce za a ƙara tura wasu jiragen yaƙi zuwa jihar domin cigaba da aikin sojin, kamar yadda babban hafsan ya bayyana a ziyararsa ga Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal.
Tags: Bello, Halilu Sububu, Musa, SOJI, Turji
Mai rahoto;Salihu Garba.
At-tajdid News.




