By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Musulmin Duniya Za Su Yi Duk Mai Yuwa Domin Kare Masallacin Qudus Mai Alfarma Tare Da Gargadin Firaministan Isra’ila NetanyahuFidan ya gargadi masu goyon bayan firaministan Isra’ila Netanyahu.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > Uncategorized > Musulmin Duniya Za Su Yi Duk Mai Yuwa Domin Kare Masallacin Qudus Mai Alfarma Tare Da Gargadin Firaministan Isra’ila NetanyahuFidan ya gargadi masu goyon bayan firaministan Isra’ila Netanyahu.
Uncategorized

Musulmin Duniya Za Su Yi Duk Mai Yuwa Domin Kare Masallacin Qudus Mai Alfarma Tare Da Gargadin Firaministan Isra’ila NetanyahuFidan ya gargadi masu goyon bayan firaministan Isra’ila Netanyahu.

Attajdid
Last updated: 2024/09/11 at 12:29 PM
Attajdid Published September 11, 2024
Share
SHARE

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce kasashen Musulmi za su yi duk abin da ya kamata don kare “alamar Musulunci” wato Masallacin Ƙudus, daya daga cikin wurare mafi tsarki ga Musulmai.”

Al’ummar Musulmi za su yi duk abin da ya kamata don kiyaye alamar Musulunci na Masallaci Mai Tsarki da ruhi iri daya,” in ji Fidan a ranar Talata yayin jawabinsa a Taron Majalisar Ministocin Harkokin Wajen Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa karo na 162.”

Za mu ci gaba da ayyukanmu na hadin gwiwa don matsa wa kasashen duniya lamba kan su yi watsi da ayyukan Isra’ila.”Haram al Sharif kuma ana kiransa da Masallacin Ƙudus, wanda ya fuskanci kutse sosai daga shugabannin masu tsattsauran ra’ayi na Isra’ila a cikin ‘yan watannin nan.

Fidan ya gargadi masu goyon bayan firaministan Isra’ila Netanyahu, yana mai cewa su ne ke da hannu wajen kisan gillar da ake yi wa Falasdinawa a Gaza.”Haka kuma za a yi musu hukunci.”

A ranar Litinin, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kuma bukaci shugabannin Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmi ta OIC da su hadu a matakin jagoranci “ba tare da bata lokaci ba” don taimakawa wajen kare Birnin Kudus daga hare-haren Isra’ila.Karfafa DangantakaDangantakar Turkiyya da Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Larabawa ta samu ci gaba sosai tun lokacin da aka kafa ta a hukumance a shekara ta 2003, wanda ke da muhimman abubuwa da dama.Wani muhimmin lokaci ya faru a watan Oktoban 2023 lokacin da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya ziyarci birnin Alkahira inda ya gana da Sakatare Janar na Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Larabawa, inda ya sake jaddada aniyar Turkiyya ta karfafa alaka da kasashen Larabawa.

An ci gaba da tattaunawa a watan Fabrairun 2024 a Ankara, inda mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar Ahmet Yildiz ya gana da mataimakin babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ambasada Hossam Zaki, wanda shi ma ya halarci taron diflomasiyya na Antalya.An fara gudanar da alaƙar ne da yarjejeniyar fahimtar juna a shekara ta 2004, kuma an ci gaba da kulla yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Larabawa a shekarar 2007.

A cikin wata fitacciyar huldar da aka yi, firaministan kasar na wancan lokaci kuma shugaban kasar na yanzu Recep Tayyip Erdogan ya yi jawabi a taron bude taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a shekarar 2011, inda ya bayyana irin kwarin gwiwar da Turkiyya ke da shi kan harkokin diflomasiyya na kasashen Larabawa da kuma karfafa dankon zumunci tsakanin Turkiyya da kungiyar kasashen Larabawa.

TRT Afarka Hausa.

At-tajdid News.

You Might Also Like

TRUMP AND CHRISTIAN GENOCIDE IN NIGERIA

TRUMP AND CHRISTIAN GENOCIDE IN NIGERIA

2025 World Sight Day: NOA Advocates Eye Healthcare Consciousness 

ZANGA-ZANGA A SOKOTO: JAMA’A NA KUKAN TSARO, GOMNATI NA DAUKAR SABON MATAKI

The 2009 ASUU Agreement and the FGN’s Endless Broken Promises

Attajdid September 11, 2024 September 11, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Jigawa Golden Star Spokesperson Turbaned As Sarkin Dawaki

Attajdid Attajdid June 1, 2025
Ministan harkokin wajen Iran Ya Magantu Akan Tattaunawa da Amurka
DG Due Process Warns Contractors Against Forgery, as Jigawa Awards N220 Billion Road Projects.
Ana barazanar mika ɗan jarida Mustafa Ayash daga Hollanda zuwa Isra’ila — zanga-zangar neman sakin sa da kare ‘yancin jarida
16 died, 3,936 Displaced By Flood In Jigawa.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?