ZANGA-ZANGA A SOKOTO: JAMA’A NA KUKAN TSARO, GOMNATI NA DAUKAR SABON MATAKI
A jihar Sokoto, Arewa maso Yammacin Najeriya, al’umma sun gudanar da zanga-zanga kan matsalar tsaro da ta addabi yankunansu. Mazauna kauyuka sun bayyana cewa a tsawon kwanaki uku a jere, ‘yan bindiga sun rika kai hare-hare tare da sace mutane ba tare da jami’an tsaro sun kawo dauki ba.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa: “Rashin kulawar da gwamnati ta nuna mana ya sa muka rufe hanyar mota don janyo hankalinta da jami’an tsaro.”
A yayin da ake cikin wannan hali, wasu al’ummar yankin sun yi ikirarin cewa gwamnatin jiha ta yi watsi da su, inda wasu mata suka bayyana irin asarar da suka yi sakamakon hare-haren. Wata mata mai suna Tunba ta ce ta rasa ‘ya’yanta guda biyar, tana mai rokon gwamnati ta samar musu da tsaro.
Hukumomin NEMA da SEMA sun tabbatar da cewa sun riga sun san da lamarin, inda daruruwan mutane suka tsere daga gidajensu suna neman mafaka a yankin Shagari. Hakiman kauyukan da abin ya shafa kuma sun roki gwamnati ta kawo daukin gaggawa domin a dawo da zaman lafiya.
A wani labarin makamancin haka, wani hatsarin kwale-kwale ya rutsa da mutanen da ke kokarin tserewa ‘yan bindiga a karamar hukumar Sabon Birni. Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutane shida, yayin da wasu kuma suka bace cikin ruwa.
A gefe guda kuma, gwamnatin jihar ta sanar da wani shirin tallafawa koyar da addinin Musulunci da kuɗin alawus na N500,000 da za a rika biyan malamai a wasu yankuna. Wannan mataki ya samu yabo daga Sarkin Musulmi da sauran shugabanni, inda suka ce zai taimaka wajen karfafa zaman lafiya da haddar Alkur’ani a tsakanin matasa.
Rahoto: M.B.S.Gama




