Gwamnatin tarayya ta cire sama da naira biliyan 256 daga rabon kudaden man fetur na wata-wata, a kashi na farko na rabin shekarar 2025 domin aiwatar da ayyukan gine-ginen bututun gas a faɗin ƙasar nan.
Binciken rahoton wata-wata na FAAC tsakanin watan Janairu zuwa Yuni ya nuna cewa adadin kuɗin da aka cire ya rika sauyawa, inda watan Yuni ya fi kowanne hawa da kashi 60.38 cikin ɗari a cikin wata guda.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke shirin sake duba tsarin cire kuɗi da kuma adana wasu kaso na kudaden shiga.
A cewar jaridar PUNCH, ayyukan da ake aiwatarwa sun shafi dukkanin yankunan siyasa guda shida na ƙasar, domin cike gibi a harkar samar da iskar gas.
An kafa majalisar kula da asusun MDGIF a 2023 karkashin shugabancin Ministan Gas, Ekperikpe Ekpo, tare da hukumar NMDPRA a matsayin mai gudanarwa.
Asusun na da nufin jawo sama da Dala biliyan 575 na jari domin bunƙasa harkar gas, ya kuma tabbatar da gina ƙarin kayayyakin more rayuwa da za su ƙarfafa kasuwar gas a Najeriya. Sai dai asusun, wanda a asali aka tsara shi ya dogara da kuɗin da ake cirowa daga kan farashin sayar da man fetur da iskar gas, sai dai yanzu ya fi dogaro ne da rabon da ake cirewa daga kuɗin gwamnati.




