Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya sanar da mutuwar Babban Hafsan Sojan Kasa na kasar Laftanal Janar Taoreed Abiodun Lagbaja bayan ya yi jinya, kamar yadda mai magana da yawun Shugaban Ƙasar, Bayo Onanuga ya bayyana a shafinsa na X ranar Laraba.
Marigayin ya rasu yana da shekara 56 kuma Shugaba Tinubu ya nada shi babban hafsan sojin kasa na kasar a watan Yunin bara.
Shugaba Tinubu ya jajanta wa iyalan marigayin da kuma rundunar sojin kasa ta kasar dangane da wannan rashi. TRT Afarka Hausa.
At-tajdid News.




