By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: CBN zai sayar wa ‘yan canji dala kan 1,580
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > CBN zai sayar wa ‘yan canji dala kan 1,580
News

CBN zai sayar wa ‘yan canji dala kan 1,580

Attajdid
Last updated: 2024/09/07 at 10:55 AM
Attajdid Published September 7, 2024
Share
SHARE

Babban Bankin Nijeriya CBN ya ce zai sayar da dalar Amurka 20,000 ga kowane ɗan canji mai rajista a kan naira 1,580 domin cike giɓin da ake da shi na dala a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje.Wannan matakin da CBN ɗin ya ɗauka shi ne na baya-bayan nan da bankin ya ɗauka domin daidaita farashin dala da naira a kasuwar canji.

Babban Bankin Nijeriya CBN ya sanar da cewa zai sayar wa ‘yan canji dala kan naira 1,580.

Bankin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarancin dalar a kasuwannin bayan fage.

Bankin ya sanar da cewa zai sayar da dalar Amurka 20,000 ga kowane ɗan canji mai rajista a kan naira 1,580 domin cike giɓin da ake da shi.Sai dai bankin ya ce bai amince ga ‘yan canjin su sayar da dalar sama da kashi ɗaya cikin 100 na kan yadda suka same ta daga CBN ba.

CBN ɗin ya buƙaci ‘yan canjin da suke da rajista kuma suka cancanta da ke buƙatar waɗannan kuɗaɗe kan su biya kuɗinsu a naira ga asusun saka kuɗi na babban bankin.

Hakazalika bankin ya ce hada-hadar biyan kuɗin da bayar da shaida da karɓa dala 20,000 ɗin duka ‘yan canjin za su iya zuwa ofisoshin babban bankin da ke Abuja ko Awka ko Kano ko kuma Legas.Wannan matakin da CBN ɗin ya ɗauka shi ne na baya-bayan nan da bankin ya ɗauka domin daidaita farashin dala da naira a kasuwar canji.

Haka kuma matakin na zuwa ne a daidai lokacin da aka rinƙa sayar da dalar a kan naira 1,670 a kasuwannin bayan fage a faɗin ƙasar.

A baya CBN ɗin ya ta ɗaukar jerin matakai domin tabbatar da cewa naira ta samu tagomashi a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje, sai dai lamarin ya ci tura, inda dalar ke ci gaba da tashi.

TRT Afrika Hausa.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid September 7, 2024 September 7, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Bola Tinubu Ya Kara Wa Kayedo Egbetokun Wa’adin Shekaru 3

Attajdid Attajdid September 3, 2024
WANENE JABOTINSKY WANDA NETANYAHU YAKE BI  KUMA YA AJIYE TAKOBINSA?
Biden Adviser Sullivan Holds ‘rare’ Talks With Top Chinese Army Official.
Jama’ar gari sun kashe DPO, sun ƙona ofishin ’yan sanda a Kano
Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?