Kungiyar Hamas ta hannun dakarunta na Kata’ib al-Qassam, tare da haɗin gwiwar mayakan Saraya al-Quds… ta ce ta kai hare-hare a sassa daban-daban na Yammacin Kogin Jordan da kuma Zirin Gaza.
A sanarwar da suka fitar… dakarun sun ce sun dasa wata babbar nakiya mai ƙarfi a kusa da shingen “Netsani Oz” da ke lardin Tulkarm, inda suka tarwatsa wata motar soja ta Isra’ila.
A wani bangare na jerin hare-haren da suka kira “Asa Musa”… an nuna bidiyon da ya bayyana yadda aka kai hari kan wata tankin Merkeva a tsakiyar Jabaliya… inda Isra’ila ta tabbatar da mutuwar sojojinta hudu.
Kungiyar ta kuma ce ta lalata tankoki biyu na Merkeva a Mafraq al-Saftawi… a ranar biyar ga watan Satumba.
Sannan ta ce ta harbo wata motar ɗaukar sojoji da makamin “al-Yasin 105” a Khan Yunis… a ranar ashirin da biyar ga watan Yuli.
A nata bangaren… hukumomin sojin Isra’ila sun tabbatar da wasu daga cikin hare-haren, sai dai suka ce suna ci gaba da kai farmaki don murkushe kungiyoyin.
Masu lura da harkokin tsaro sun ce… waɗannan hare-haren na nuna yadda kungiyoyin ke ƙoƙarin matsa lamba a lokaci guda daga Gaza… da kuma Yammacin Kogin Jordan.
Hare-haren na ci gaba ne a ƙarƙashin yakin da aka fi sani da “Tufanul-Aqsa.”
Ya fara ne a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023… ya kuma janyo mummunar asarar rayuka da lalacewar ababen more rayuwa a Gaza.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




