Tsawa ta hallaka yara 14 da jikkata 34 a Uganda
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
Yara aƙalla goma sha hudu ne suka mutu a arewacin ƙasar Uganda bayan da tsawa ta faɗa musu.
Ƴansanda sun ce akwai kuma wasu yaran talatin da huɗu da ta ji wa rauni, inda bakwai daga cikinsu suke cikin mawuyacin hali a asibiti.
Lamarin ya faru ne a jiya Asabar da yamma a lokacin ibada a sansanin ‘yan gudun hijirana Palabek a gundumar Lamwo.
Sansanin na ɗauke da ‘yan gudun hijira na Sudan ta Kudu kusan dubu talatin da shida.
A kwanan nan an riƙa yin mamakon ruwan sama da tsawa da walkiya sosai a yankin.




