Kotu Ta Dakatar Da KANSIEC Karbar N10m Da N5m Kudin Tsayawa Takarar Chairman Da KansilaWata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) karbar Naira Miliyan10 da Miliyan 5 daga hannun ‘yan takarar shugabancin ƙaramar Hukumomi da kuma Kansiloli a zaben kananan hukumomi da ke tafe.
Alkalin kotun Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin a ranar Laraba.Solace Base ta ruwaito cewa Action Peoples Party (APP), Action Democratic Party (ADP) da Social Democratic Party (SDP) ne suka shigar da karar Kotu.
Hukumar zabe Mai zaman kanta ta Jihar Kano KANSEIC ce ake tuhuma a cikin lamarin.
Mai rahoto;Salihu Garba.
At-tajdid News.




