By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamnatin Jihar Kano ta goyi bayan ƙudurin haramta auren jinsi
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Gwamnatin Jihar Kano ta goyi bayan ƙudurin haramta auren jinsi
News

Gwamnatin Jihar Kano ta goyi bayan ƙudurin haramta auren jinsi

Attajdid
Last updated: 2025/09/13 at 6:03 PM
Attajdid Published September 13, 2025
Share
SHARE

Gwamnatin Jihar Kano ta goyi bayan ƙudurin haramta auren jinsi

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar bayan taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 31.

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da miƙa wa Majalisar Dokokin jihar wani ƙudiri na haramta auren jinsi da sauran abubuwan da ake ganin ba su da kyau a tsarin addinin Musulunci da na al’ada.

 

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar bayan taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 31.

 

Gwamna Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kare martabar Musulunci da kuma al’adun Jihar Kano. Ya bayyana ƙudurin dokar a matsayin kariya ga mutuncin jihar.

 

“Babu wani dalili ko yanayi da zai sa mu bar ayyukan da suka saɓa wa addininmu da al’adunmu su yi katutu a Kano, wannan gwamnati wajibi ne ta kare mutuncin al’ummarmu,” in ji shi.

Ƙudirin dokar ya tanadi haramta auren jinsi da sauran ayyukan da ake kira maɗugo da luwaɗi a cikin gida, waɗanda haramtattu ne a tsarin Shari’ar Musulunci.

 

Idan an zartar da ƙudurin, masu laifin da aka samu da hannu ko haɓaka irin waɗannan ayyukan za su fuskanci hukunci mai tsauri na shari’a.

 

Gwamna Yusuf ya bayyana ƙwarin gwiwarsa na cewa ‘yan majalisar dokokin jihar za su bai wa kudurin mahimmanci da kuma gaggauta amincewa da shi bisa la’akari da mahimmancinsa ga kyawawan halaye da zamantakewar al’ummar Jihar Kano.

 

Mai rahoto

Mustapha Garba Usman

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid September 13, 2025 September 13, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai A Jarabawa

Attajdid Attajdid May 18, 2025
Kotu Ta Dage Ci Gaba Da Sauraren Shaidu A Shari’ar Da Ake Zargin Matashin Da Ya Cinnawa Masallata Wuta A Kano
Gina Jamiyya Ne A Gabanmu Ba Zaɓar Wanda Zai Yi Takarar Ba – ADC
Masana sun ce wani makeken dutse da yafi komi girma ya taho a guje zai wuce ta saman duniya ranar Juma’a mai zuwa Masana sararin samaniya sunyi hasashen cewa wani makeken dutse da yafi komi tsawo da girma a duniya zai wuce ta saman duniya (Earth) a ranar Juma’a mai zuwa.
Takaitattun Abubuwan da Suka Faru a Khan Yunis Dake Gaza.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?