Masana sunyi hasashen girman dutsen mai suna 7335 (1989 JA) ya kai tsawon mil 1.1 wato Kilo mita 1.8 kuma yana tafe a guje ya tunkaro Duniyar Earth zai wuce.Hukumar kula da sararin samaniya wato NASA tace dutsen “mai yuwuwar haɗari ne ga duniya” amma babu tabbas ganin cewa akwai abubuwa da dama da suka tunkaro duniya amma dai a wannan shekarar wannan dutsen shine mafi girma da zai wuce ta saman duniyar mu.
Jaridar. Ng Hausa ta ruwaito NASA tace da fari dutsen zai bawa duniya tazarar mil 2.5 million wato 4 million kilometres wato akalla tazarar nisan dake tsakanin Duniyar Earth da wata sau 10 amma daga bisani zai rika zuwa kusa-kusa da duniya kuma wajajen karfe 2:26 na ranar Juma’a zai yi daf da duniya kana ya wuce a guje gudun da ya ninka gudun fitar harsashin bindiga sau 18.
Me zaku ce?




