Asibitin Shifa ya tabbatar da mutuwar mutane 9 ciki har da yara sakamakon wani harin Isra’ila a gidan dake unguwar Tel al-Hawa, kudu maso yammacin Gaza.
Cibiyar bada agajin gaggawa ta Gaza ta ce mutane 4 sun mutu, wasu kuma sun ji rauni a wani hari kan gidaje a unguwar Sheikh Radwan, arewacin Gaza, haka kuma an samu raunata a wani hari kan tantin ‘yan gudun hijira a yankin Mawasi, Khan Younis.
A asibitin Nasser na Khan Younis, mutane 5 daga cikin masu neman tallafi sun rasa rayukansu sakamakon harbin dakarun Isra’ila.
Asibitocin Gaza gaba ɗaya sun tabbatar da mutuwar mutane 20 tun daga safiyar yau, daga cikinsu kuwa akwai 5 daga masu neman tallafi.
Rahotanni daga Aljazeera sun nuna cewa sojojin Isra’ila suna gudanar da tarwatsa gine-gine a Jabaliya, arewacin Gaza.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




