Rundunar sojin Isra’ila ta kasa mamayar ko da ƙauye ɗaya a Lebanon tun bayan da ta fara kai hare-harenta cikin ƙasar a watan Satumba, a cewar ƙungiyar Hezbollah.
“Bayan shafe kwana 45 ana mummunan yaƙi, har yanzu maƙiya sun kasa mamayar ko da ƙauye ɗaya a ƙasar Lebanon,” kamar yadda mai magana da yawun ƙungiyar Hezbollah, Mohammad Afif ya shai da taron manema labarai a kudancin Beirut, inda Isra’ila ke ta kai hare-haren sama a wajen.
Yakin da Isra’ila ke yi a Gaza wanda a yanzu ya shiga kwana na 402 ya kashe akalla Falasdinawa 43,603 da jikkata 102,929, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra’ila ta kashe mutum 3,136 tun Oktoban bara.
At-tajdid News.




