A ranar Juma’a da ta gabata kungiyar WOPAN ta gwangwaje mutanan garin Garinmalam da gyaran masallacin Juma’a na kungiyar Jama’atut Tajdidil Islamy (JTI) tare da tallafawa masu bukata ta musamman na yànkin.
An gudanar da bikin Bude masallacin juma’ar na Jama’atut Tajdidil Islamiyya (JTI) wanda kungiyar Mata manoma ta sabunta gininsa tare da rabon kekunan ga masu bukata ta musamman a matsayin bikin ranar (disabled) masubukata ta musamman ta duniya.
Tare da gudanar da addu’oi na musamman ga al’ummar yankin da kuma jagororinta, an sami halartar masu fada-a-ji na yankin da ya hada masu sarautar gargajiya da malamai da kuma ‘yan siyasa.
Mai rahoto;
Mal. Yahaya Dumaji.
At-tajdid News.






