A wani rahoto da At-tajdid News ta samu yankin gabas ta tsakiya dakarun Al-Qassam sun kai hari kan wani jirgin ruwa dauke da sojoji biyu a unguwar Shujaiya da ke gabashin birnin Gaza.
Dakarun Al-Qassam sun kai harin gwiwa da rundunonin Quds sun kai hari a wani wuri da ke da suke da iko a kudancin yankin Al-Qaizan a Khan Yunis. Daga bisani suka hadu da sojojin Isra’ila a cikin motoci inda suka kai musu a yankin Al-Satar da ke Khan Yunis.
Asibitocin Gaza na karbar wadanda suka samu raunuka ciki har da yara kanana ana kwantar da su a kasa a tantinan likitoci saboda yawan wadanda suka jikkata sakamakon ci gaba da yakin da ake yi na kokarin kawar da mazauna yankin Gaza daga yankin.
Babban Hafsan Hafsoshin Isra’ila ya bayyana cewa “Mun riga mun mallaki kashi 75% na zirin Gaza, kuma a cikin kwanaki masu zuwa za mu san ko akwai yarjejeniya ko a’a”.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




