Majalisar zartarwar Nijeriya ta soke wasu ma’aikatu na kasar ta kuma hade ayyukan wasu ma’aikatun, sannan an kirkiri sabuwar ma’aikata.
An soke Ma’aikatar Nija Delta da ma’aikatar ci gaban wasanni kuma za a samar da ma’aikatar ci gaban yankuna da zata kula da hukumomin ci gaban sheyoyi, hukumar wassanni ta kasa zata karbe aiyukan ma’aikatar wassanni kuma an hade ma’aikatar yawan bude ido da ma’aikatar al’adu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X ta ce an ɗauki matakan ne a zaman majalisar zartarwar ƙasar a ranar Laraba, inda Shugaba Tinubu ya jagoranci zaman.
At-tajdid News.




