Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da sakon ta’aziyya mai cike da alhini ga Shugaban Ghana, John Mahama, da al’ummar kasar, sakamakon hatsarin jirgin sama da ya yi sanadin mutuwar ministoci biyu na majalisar zartarwa da wasu mutane shida.
A cewar rahotanni, hatsarin ya yi sanadin mutuwar Ministan Tsaro na Ghana, Edward Omane Boamah, da Ministan Muhalli, Ibrahim Murtala Muhammed, tare da wasu mutane shida, inda aka bayyana cewa suna kan aikinsu na gwamnati lokacin da hatsarin ya faru.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a jiya, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin Najeriya da al’ummarta na tare da Ghana a wannan lokaci na jimami da alhini.
Shugaba Tinubu ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga kasar Ghana, tare da jajanta wa iyalan mamatan da daukacin al’ummar kasar, yana mai cewa su Kara hakuri da juriya, ganin cewa wadanda suka rasu sun mutu ne a yayin gudanar da hidimar kasa cikin kishin kasa da sadaukarwa.
Nura Abubakar Musa
At’tajdid News




