By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Akwai yuyuwar Dr. Abdullahi Umar ganduje daga Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa zai zama jakadan Najeriya a guda cikin kasashen Afrika.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Akwai yuyuwar Dr. Abdullahi Umar ganduje daga Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa zai zama jakadan Najeriya a guda cikin kasashen Afrika.
News

Akwai yuyuwar Dr. Abdullahi Umar ganduje daga Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa zai zama jakadan Najeriya a guda cikin kasashen Afrika.

Attajdid
Last updated: 2024/08/16 at 4:03 PM
Attajdid Published August 16, 2024
Share
SHARE

Rahotanni sun nuna Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yi wa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, tayin muƙamin jakada a ɗaya daga ƙasashen Afrika, kamar yadda wata majiya mai tushe ta tabbatar.

Kazalika, majiyar ta ce shugaban ya wakilta shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya sanar da Ganduje.Idan zamu iya tunawa an naɗa Ganduje, a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a ranar 3 ga watan Agusta 2023, biyo bayan murabus ɗin da Abdullahi Adamu yayi A cewar majiyar Akpabio, ya shaida wa Ganduje tayin shugaban ƙasar na da nufin ceto shi daga shari’ar cin hanci da rashawa da yake fuskanta a Kano game da faifan bidiyon Dala na shekarar 2018.

Ya ce bidiyon ya janyo masa ba’a da gori a bainar jama’a, tare da matarsa da ɗansa da kuma sauran masu hannu cikin lamarin na sama da Naira biliyan 50.Sai dai wata majiya, ta ce Ganduje ya ƙi amincewa da tayin, inda ya bayyana cewa zargin ƙarya ne, kuma zai yi nasara a shari’arsa a kotu wanda shugaban Tinubu da kansa ya sanar da Ganduje shiri na diflomasiyya tare da ba shi damar zaɓar wata ƙasa a Afirka.Wata majiya ta kusa da Ganduje ta ce abin da shugaba Tinubu, ya fi so shi ne ya naɗa shi Jakadan Nijeriya a ƙasar Chadi, duba da cewar ya taɓa yin aiki a Ndjamena a matsayin babban sakataren hukumar kula da tafkin Chadi tsakanin 2009 zuwa 2011.

Jaridar Daily Nigeria ta ruwaito cewa kwanaki kaɗan bayan Shugaba Tinubu ya sanar da matakin ga Ganduje, an aike masa da wasiƙar wa’adi game da buƙatar ya gudanar da babban taron majalisar jam’iyyar APC na ƙasa.Wasikar mai ɗauke da kwanan wata 9 ga watan Agusta, da sa hannun Shugaban Hadiman Tinubu, Femi Gbajabiamila, ta sanar da Ganduje cewa shugaban ƙasa zai samu halartar taron Majalisar Jam’iyyar a ranar 8 zuwa 19 ga Satumba, 2024.

Ko da aka tuntuɓi mai magana da yawun Ganduje, Edwin Olofu, ya ce mai gidansa bai yi masa bayani kan batun ba amma ya tabbatar da amincewar shugaban ƙasa na a gudanar da babban taron jam’iyyar.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid August 16, 2024 August 16, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Tattalin Arzikin Kasar Syria na Kara Bunkasa a Yayin da Wasu ‘Yan Kasar Suke Cigaba da Dawowa Kasar 

Attajdid Attajdid January 9, 2025
Jigawa Border Community Group Flagged-off Tree Planting Campaign To Tackle Environmental Degradation
Bayani kan Masjidul Aqsah tare da Malam Aminu Aliyu Gusau.
FG Begins Public Sensitization On Empowerment Opportunities In Jigawa
Israeli lawmaker urges world to act to prevent ‘genocide’ in West Bank
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?