Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karyata cewa akwai rigima ko wata matsala tsakaninsa da jagoran jam’iyyar NNPP, Dr.Rabiu Musa Kwankwaso.
A cewarsa “mun yi shekara 40 tare da Kwankwaso kuma ba wata rigimar da aka taɓa ji tsakaninmu, sai yanzu ne za mu yi hakan?”kamar yadda BBC Hausa tafitar a ranar Alhamis din data gabata.
Sannan Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya kara da cewa ce-ce ku-cen rigimar siyasa ba shi ne a gabansa ba, illa yi wa jama’a aikin da zai amfane su.
Mai Rahoto;
Zainab Sulaiman Naibawa.
At-tajdid News.




