Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya gargadi shugabannin duniya a Babban Taron Zauren MDD kamar yadda majiyarmu ta yankin gabas ta tsakiya ta bayyana cewa, Lebanon “tana cikin hadari” daga hare-haren Isra’ila kuma bai kamata su bar ta ta mayar da kasar kamar “wata Gaza” ba.
A wata ganawa da ya yi da manema labarai a shekara ta 2020 Guterres ya ce, matsayin Majalisar Dinkin Duniya a fayyace yake dangane da dokokin duniyar da kuma matsayin Falasdinu.
Guterres ya ce, har yanzu babu abin da ya sauya dangane da matsayinsu na samun kasashe biyu tsakanin Israila da Falasdinu a kan iyakokin shekarar ta 1967.
At-tajdid News.




