Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda yace baya ga tallafin dabbobi da gwamnati zata bawa daliban su 340 zakuma ta Kara musu da kudi domin su sami damar kula da dabbobin yadda ya kamata.
Daliban da suka samu horo kan kula da tsirrai, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati zata raba musu injinan ban ruwa da wheelbarrow da injin feshin maganin kwari da sauran kayan kula da tsirrai.
Daga nan yayi kira ga dalib
an da suka amfana da Kada suyi wasa da wannan dama da suka samu inda ya jadda cewa gwamnati zata dinga bibiyarsu domin tabbatar da basu juyar da dabbobin ta hanyar da bata kamata ba. Radio Kano.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




