Rahotonnin da muka samu daga Jahar Maduguri ya tabbatarwa majiyar At-tajdid News an sami Ambaliyar ruwan da misalin karfe karfe uku 3:00pm na dare ta aukune a birnin Maidugurin jihar Borno rahotonni sun tabbatar mana cewa jama’ar birnin sun shiga cikin mawuyacin hali. Masu nazarin yadda al’amarin, ya afkune sandiyar cushewar magudanan ruwa kamar yanda majiyarmu ta tabbatar mana.
wakilinmu ya sami zantawa da wasu daga cikin mazauna wanna yankin ta wayar tafi-da-gidanka sun tabbatar masa da faruwar al’amarin inda suka tabbatar masa cewa unguwanni da dama sun sami ambaliyar ruwa.
Ambaliyar tafi shafar unguwannin Gwange, kofar-Shehu, Shahuri da Abbagada da sauransu.
Mai Rahoto Mujahid Muhammad Tasiu.
At-tajdid News.




