Human Rights Watch: Sojojin Isra’ila da ‘yan kwangila da Amurka ke marawa baya sun kafa tsarin rarraba kayan agaji na soji a Gaza.
Ta bayyana tsarin rarraba kayan agaji a Gaza ya rikide zuwa zubar da jini na yau da kullum.
Sun kara da cewa mummunan yanayin ya samo asali ne sakamakon amfani da yunwa da Isra’ila ke yi wa fararen hula a matsayin makamin yaki.
Sun ce dole ne duniya ta matsawa Isra’ila lamba da ta dage takunkumin hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




