By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Jirgin Ruwan Oruc Reis na Turkiyya ya Isa Somalia Don Binciken Albarkatun Mai da Iskar Gas
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Jirgin Ruwan Oruc Reis na Turkiyya ya Isa Somalia Don Binciken Albarkatun Mai da Iskar Gas
International News

Jirgin Ruwan Oruc Reis na Turkiyya ya Isa Somalia Don Binciken Albarkatun Mai da Iskar Gas

Attajdid
Last updated: 2024/10/27 at 10:50 AM
Attajdid Published October 27, 2024
Share
SHARE

Jirgin ruwan Turkiyya mai bincike, Oruc Reis ya isa gaɓar tekun Somalia don gudanar da bincike kan albarkatun mai da iskar gas, in ji Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa na Turkiyya, Alparslan Bayraktar.

 

“Oruc Reis ya isa wajen da zai yi aiki bayan tafiyar keta nahiyoyi,” in ji Bayraktar a saƙon da ya wallafa a shafin X ranar Juma’a.

 

Ministan tare da Shugaban Ƙasar Somalia Hassan Sheikh Mahamud za su halarci bikin tarbar jirgin.

 

A farkon watan nan ne jirgin ya tafi Somalia don gudanar da binciken mai da albarkatun iskar gas a yankuna uku da Turkiyya ta samu lasisin neman mai.

 

Oruc Reis zai yi aikin binciken mai da iskar gas da fasahar 3-D a gaɓar tekun Somalia.

 

Ana sa ran aikin zai shafe watanni bakwai yana aiki da zai ƙunshi tattara bayanai game da mai da iskar gas.

 

Za a yi nazari kan bayanan da aka samu a Ankara don bayyana a waɗanne wurare ne za a iya hako man.

 

A farkon wannan shekarar, Turkiyya da Somalia sun sanya hannu kan yarjeniyoyin fahimtar juna a tsakanin ma’aikatu da gwamnatocinsu.

 

A ƙarƙashin waɗannan yarjeniyoyi, Kamfanin Mai na Turkiyya, ya samu lasisin binciken albarkatun mai a wurare uku da ke tekun Somalia.

 

Ma’aikatar na shirin gudanar da bincike a dukkan wuraren uku, wanda kowane na girman murabba’i 5,000.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 27, 2024 October 27, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Zulum Approves N730 Million Scholarship for Indigenous Student

Attajdid Attajdid December 3, 2024
Mutum 7 Sun Mutu Sakamakon Hadarin Mota A Titin Zariya-Kano
MINISTAN TSARON ISRA’ILA YA YI BARAZANA GA YEMEN
Isra’ila ta Kai Sabbin Hare-hare ta Sama a Kudancin Beirut
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kira da a sake fasalin tsarin ilimi don ya zo daidai da muradun fasahar zamani, kere-kere da cigaban zamani
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?