Isra’ila ta kashe Falasdinawa akalla bakwai tare da raunata wasu da dama a hare-haren da ta kai ta sama a Gaza da ta yi wa ƙawanya.
Sojojin Isra’ila sun kai hari kan wata rumfa da ke gefen titi da ake sayar da kayayyaki a yankin Qizan Abu Rashwan da ke kudancin Khan Younis, inda suka kashe Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
A wani harin da Isra’ila ta sake kai wa, wata majiyar lafiya ta shaida wa Anadolu cewa Falasdinawa uku ne suka mutu, wasu goma kuma suka jikkata, yawancinsu kananan yara, a wani harin da aka kai ta sama a wani gida da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.
A cewar majiyar, daya daga cikin wadanda suka jikkata ya rasu kafin a isa Asibitin Al-Awda da ke Nuseirat, yayin da wasu goma suka samu raunuka.
An kai wasu “sassan jikin” mutum biyu da abin ya shafa asibitin shahidan Al-Aqsa, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana.
Yakin da Isra’ila ke yi a Gaza wanda a yanzu ya shiga kwana na 404 ya kashe akalla Falasdinawa 43,665 da jikkata 103,076, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra’ila ta kashe mutum 3,287 tun Oktoban bara.TRT African Hausa.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu.
At-tajdid News.




