By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: {AMBALIYAR RUWA} MUTUM 129 SUN MUTU YAYIN DA SAMA DA 120 SUKA JIKKATA A NIJAR.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > {AMBALIYAR RUWA} MUTUM 129 SUN MUTU YAYIN DA SAMA DA 120 SUKA JIKKATA A NIJAR.
International News

{AMBALIYAR RUWA} MUTUM 129 SUN MUTU YAYIN DA SAMA DA 120 SUKA JIKKATA A NIJAR.

Attajdid
Last updated: 2024/08/20 at 5:41 PM
Attajdid Published August 20, 2024
Share
SHARE

Iftila’in ambaliyar ruwan sama a Nijar ya yi sanadin mutuwar mutum 129, yayin da wasu mutum 126 kuma suka jikkata, a cewar Hukumar shirye-shirye da gargadi da kuma taƙaita aukuwar bala’o’i tare da kare al’umma (DPA/GC) a ƙasar. 

Mutane da dama sun mutu a ambaliyar ruwa a Nijar, yayin da wasu kuma suka jikkata / Hoto: AFPMummunan iftila’in ambaliyar ruwa a Nijar ya yi sanadin mutuwar mutane da dama yayin da wasu kuma suka jikkata tun da aka shiga lokacin daminar bana a ƙasar.

Hukumar shirye-shirye da gargadi da kuma takaita aukuwar bala’o’i tare da kare al’umma (DPA/GC) a Nijar, ta ce ya zuwa 12 ga watan Augusta, 2024 iftila’in ya yi sanadin mutuwar mutum 129, yayin da wasu mutum 126 kuma suka jikkata.Rahotanni sun yi nuni da cewa, al’ummomi 28,000 ne iftila’in ya shafa, yayin da gidaje 23,619 suka rushe sannan an yi asarar dabbobi 16,000, kamar yadda kafar yada labarai ta Actuniger ta rawaito.

Yawan adadin da ɓarnar ta haifar ya ƙaru sosai idan aka kwatanta da adadin da ministar ayyukan jinƙai da takaita aukuwar bala’o’i a Nijar, Madam Aissa Laouan Wandarama ta bayyana ya zuwa ranar 7 ga watan Agusta.

Rahoton bayanan da aka tattaro a lokacin ya yi nuni da cewa, mutum 94 ne suka mutu, daga ciki an rasa 44 daga kai-tsaye sakamakon ambaliyar ruwan, yayin da 50 kuma suka mutu a ruftawar gidaje.

Kazalika adadin mutanen da lamarin ya shafa a lokacin ya kai 137,156, inda gidaje 14,045 suka rushe sai kuma ɓukkoki 502 sun lalace.

An kuma yi asasar dabbobi 15,470, daga ciki akwai ƙananan dabbobin gida 13,981 da kuma manya 297.Sannan ambaliyar ta shafe kadada 2,763 na gonakin noma a Nijar, inda aka yi asarar ton 17,495 na kayan amfanin gona tare da jikkata mutane 93.

Rahotannin baya-bayan nan dai sun nuna yadda iftila’in ya haifar da mummunar barna a kusan dukka faɗin yankunan Nijar, inda ta shafi ababen more rayuwa tare da katse hanyoyin tafiye-tafiye a ƙasar.Ƙididdigar hasashen yanayi ta yi nuni da cewa akwai yiwuwar iftila’in ambaliyar ruwa a shekarar 2024 a yankunan Yammaci da tsakiyar Afirka ya zarce na shekarun baya.Ta kuma ce hakan zai ta’azzara yanayin da al’ummomi ke ciki matukar ba a ɗauki matakan da suka kamata ba bisa ga tsarin kariya da muhimman matakan takaita tasirin sauyin yanayi da hukumomi suka bayar.

TRT Afrika

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid August 20, 2024 August 20, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Tallafin Kanyan Amfani da Aka Kaiwa Wadanda Ambaliyar Ruwan Maiduguri ta Shafa Daga Kungiyar Jama’atut Tajdidil Islamy (JTI)

Attajdid Attajdid November 6, 2024
Gwamnatin Jihar Sokoto ta raba tallafi ga iyalan da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a garin Rinaye, karamar hukumar Shagari.
Kotun kolin Ghana ta yi watsi da hukuncin da kakakin majalisar dokokin ƙasar ya yanke a ranar 17 ga watan Oktoba, da ya kori wakilai huɗu daga majalisa.
AN FARA CIRE TSAMMANIN MUTANAN DA KUNGIYAR HAMAS TA KAMOSU A HARIN 7 GA WATAN OKTOBA 2024
Takaitattun Abubuwan da Suka Faru a Khan Yunis Dake Gaza.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?