Dazu nake fadawa wasu abokaina cewa, nan da shekara daya idan hukumomi ba su yi da gaske ba, to, za a shiga matsanancin rashin ababan zirga zirga a Kano duk da dai yanzu ma ana dandanawa.
Na lura yanzu baburan Adaidaita suna yankewa saboda matsananciyar tsada da suka yi, ana maganar sabo ya haura Naira Miliyan uku, yayin da duk tsohon da ya mutu sai dai a fasa shi ‘yan gwangan su sa shi cikin kadarar su. Hayis da Taxi suke neman zama tarihi, ba a maganar Achaba da take zaman haramun a dokar Jihar Kano.
Akwai abin tausayi yadda mutane suke dandana kudarsu wajen samun ababan hawa musamman idan aka taso daga kasuwa, dazu wani ya fada min cewa, tun daga kasuwar kwari sai da suka zo har masallacin Juma’a a kasa sannan suka sami abin hawa, ba a maganar dalibai ‘yan makaranta dake kara fiye da awa daya a yayin zuwa da komawa gida.
Alhamdulillahi! Dazu na ga Mai girma Gwamna yana shaidawa ‘yan kungiyar Kwadago cewa, gwamnati na shirin samar da ababan hawa na zirga zirga masu amfani da makamashin gas, ba shakka wannan abin yabawa ne. Abba ka cika Gwarzo…. Amma dai gaskiya al’amarin ya wuce haka. Akwai bukatar manyan ‘yan kasuwa su daure su saka hannu wajen tallafawa wannan al’ummar wajen samawa dimbin matasanmu abin dogaro da kai da kuma fitar da al’ummarmu daga wannan halin kaka ni ka yi, kuma ya zama ga lada ga la’ada.
Ina fatan wannan koken ya kai kunnen masu ruwa da tsaki cikin wannan sha’anin, kuma su yi abin da ya dace.
Ali Baba
28/11/2024.
At-tajdid News.




