By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: ‘Yan Nijeriya na da Zaɓin Sayen Litar Fetur a Kan N1000 ko Iskar Gas ta CNG a Kan N200: Tinubu
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > ‘Yan Nijeriya na da Zaɓin Sayen Litar Fetur a Kan N1000 ko Iskar Gas ta CNG a Kan N200: Tinubu
News

‘Yan Nijeriya na da Zaɓin Sayen Litar Fetur a Kan N1000 ko Iskar Gas ta CNG a Kan N200: Tinubu

Attajdid
Last updated: 2024/10/25 at 3:16 AM
Attajdid Published October 25, 2024
Share
SHARE

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yaba wa kamfanin makamashi na NIPCO bisa sanya hanayen-jari a kan harkokin tsukakkiyar iskar gas wato Compressed Natural Gas (CNG) yana mai cewa hakan zai bunƙasa harkokin kasuwancin ƙasar.

 

Ya yaba wa kamfanin ne ranar Talata a lokacin da shugabanninsa suka kai masa ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, kamar yadda kakakin shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya bayyana a sanarwar da ya fitar .

 

Shugaba Tinubu ya ce rawar da NIPCO yake takawa a harkokin makamashin Nijeriya tana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ganin ‘yan ƙasar sun rungumi CNG a matsayin muhimmin zaɓi kuma mai rahusa idan aka kwatanta da fetur.

 

“Masu amfani da ababen hawa a Nijeriya suna da zaɓin sayen lita ɗaya ta fetur a kan N1,000 ko kuma kwatankwacinta wato kyubik mita ɗaya ta gas a kan N200. Kazalika mun sauƙaƙa wa masu ababen hawa na haya ta yadda za su iya sauya ababen hawansu daga masu amfani da fetur zuwa masu amfani da gas a kyauta,” in ji Shugaba Tinubu.

 

CNG: Abin da ya kamata ku sani game da makamashin iskar gas da ya fi fetur araha

 

Shugaban Nijeriya ya ce amfani da CNG yana da matuƙar muhimmanci saboda ba ya gurɓata muhalli kuma yana da araha.

 

A nasa ɓangaren, shugaban kamfanin NIPCO, Mr Ramesh Kasangra, wanda ya jagoranci tawagar jami’an kamfanin, ya jinjina wa Shugaba Tinubu bisa jajircewarsa wajen goyon bayan fannin makamashi na CNG.

 

Ya ce kamfanin NIPCO zai kyautata alaƙa da gwamnatin Nijeriya domin tabbatar da ɗorewar ƙudurinta na samar da makamashi mai araha da tsafta.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid October 25, 2024 October 25, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Dokar ta Baci a jahar Jigawa kan fannin ilimi

Attajdid Attajdid August 26, 2025
Qassam da Saraya Al-Quds Suna Cigaba da Kai Hare-hare Masu Zafi Kan Yahudawan Sahyoniyya
An zaɓi Sidi Ould a matsayin sabon shugaban Bankin Afirka
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kasa Super Eagles wacce ta ƙunshi zallan yan wasan da ke taka leda a Najeriya, tayi rashin nasara a wasan ta na farko na gasar cin kofin tamaula na ƙasashen nahiyar Afrika a hannun takwararta na ƙasar Senegal da ci daya da nema. Manazarta al’amurra wasan ƙwallon ƙafa na kallon rashin nasara a matsayi wata yar manuniya da ke nuna irin koma-baya da kuma siyasa da ta dabaibaye al’amurran zaɓen yan wasa da zasu wakilci Najeriya a wannan gasa. Alal misali, da dama daga cikin manazarta da suka kalli wasan sun nuna damuwa kan yadda masu ruwa da tsaki suka ajiye shahararren ɗan wasan Kano Pillarss Rabiu Ali Pele bisa hujjar shekarun haihuwa duk da cewa yana kan ganiyyar sa na wasa a gasar Firimiya Lig ta ƙasa, hasali ya kasance ɗan wasa daya tilo da ya kafa tarihin cin mafi yawan kwallayeya gasar ta Firimiya Lig. A sauran wasan gasar da aka fafata a rukunin da Najeriya ke ciki, an tashi daga wasa kowacce ƙungiya na da ci daya tsakanin Congo da Sudan, abin da ke nuni da cewa zuwa yanzu Najeriya ce ta karshe rukunin na ‘D’, kuma Ƙungiyoyi biyun da suka fi yawan maki sune zasu haura zuwa zagaye na gaba na gasar. A wasannin da za’a fafata a wannan rana, Burkina Faso za ta kara da jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, sai kuma wasa tsakanin Mauritania da Tanzania. A wani labarin kuma, Wata kotu a Ingila ta bayar da belin tsohon ɗan wasan Arsenal, Thomas Partey bayan tuhumar sa bisa zargin laifukan cin zarafin wasu mata. An zargi ɗan wasan na Ghana da yi wa wasu mata biyu fyaɗe tare da cin zarafin wata daban. Lamarin da ake zargi ya faru ne a tsakanin shekara ta 2021 zuwa 2022 lokacin da yake taka leda a Arsenal. Daga cikin hukunce-hukuncen da kotun ta yanke masa, ta hana Partey yi wa kowace daga cikin matan magana, sannan dole ya sanar da ƴansanda idan zai canja gida ko zai yi
DG Due Process Warns Contractors Against Forgery, as Jigawa Awards N220 Billion Road Projects.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?