By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamnatin Tinubu ba ta Aiwatar da Kasafin Kudin Bara ba da Kyau – Majalisar Dokoki
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Gwamnatin Tinubu ba ta Aiwatar da Kasafin Kudin Bara ba da Kyau – Majalisar Dokoki
News

Gwamnatin Tinubu ba ta Aiwatar da Kasafin Kudin Bara ba da Kyau – Majalisar Dokoki

Attajdid
Last updated: 2025/01/10 at 11:45 AM
Attajdid Published January 10, 2025
Share
SHARE

Majalisar dokokin Najeriya ta bayyana damuwa game da babban rashin daidaito tsakanin kudaden da akan kashe wajen ayyukan raya kasa da wadanda akan kashe don gudanar da ayyukan ma’aikatu na yau da kullum a kasafin kudin bara.

 

‘Yan majalisar sun yi nuni da yadda aka yi kwauron sakin kudi don aiwatar da manyan ayyukan raya kasa ga ma’aikatu da sassa da hukumomin gwamnati.

 

‘Yan majalisar dokokin sun ce abin da aka samu bai taka kara ya karya ba, kuma ba zai kai a ce an gudanar da ayyukan yadda ya dace ba a kasafin kudin na bara.

 

Daya daga cikin ‘yan majalisar Injiniya Satomi Ahmed, ya shaida wa BBC cewa an yi shirin aiwatar da karashen kasafin kudin na bara har zuwa watan Yunin bana, ta yadda za a rika aiwatar da shi tare da na wannan shekara.

 

Yace : “Babbar damuwar ita ce rashin fitar da kudaden da ya kamata a yi manyan ayyuka na ci gaban kasa, rashin hakan shi ne ya haifar da halin da Najeriya ke ciki, da rashin ci gaban gwamnati da matsalolin da ta ke fuskanta.

 

Ba a bai wa ma’aikatu daban-daban kudaden aiwatar da ayyuka na musamman, kamar fannin noma da ta ttalin arziki, da ma’aikatar raya yankin Arewa maso yammacin Najeriya ba.

 

Wasu ma’aikatun sun samu kashi 40, wasu kuma kashi 30 cikin 100, kai akwai wasu ma da ba su samu kashi 20 ba a kasafin kudin shekarar 2024,” in ji Satomi.

 

 

Ya kara da cewa fannin tsaro kamar hukumar leken asiri ta DSS, ma an samu wannan tsaikon, kuma hakan ya janyo musu koma baya na aiwatar da ayyukansu.

 

Wannan ne dalilin da ya sa majalisar dokokin Najeriya, ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya san halin da ake ciki, da kuma bada damar ci gaba da ayyukan a cikin shekarar nan ta 2025, duk da ita ma shekarar na da na ta kasafin kudin, kuma ya amince da hakan.

 

Shin ko yaya za a gudanar da ayyukan da ba a kammala a kasafin kudin 2024 ba, alhalin kasafin kudin 2025 na nan?

 

Sai Satomi ya ce: “Babu abin da zai sauya, tun da daman ai ayyuka ne da ba a kammala ba don haka ci gaba da su za a yi, ana kuma yin sababbin ayyukan da za a yi na kasafin kudin bana. Kuma shugaban kasa ya amince da kara wa’adin ci gaba da ayyukan.”

 

Satomi ya ce za a ga sauyi a kasafin kudin bana, ta hanyar inganta yawan man fetur da ake fitarwa da samun kudaden haraji da hanyoyin samun kudi ta fannin hukumar shige da fice ta Najeriya.

 

Za kuma su tabbatar an yi amfani da kowanne kudi da aka ware na yin ayyuka a kasafin kudin bana, ba tare da sun bada damar da mutane za su ce sun zama ‘yan amshin shata ba.

 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu lura da al’amura a Najeriya ke nuna damuwa kan dimbin bashin da gwamnati ke ci a ciki da karbowa a  wajen kasar, da kuma take fakewa da cewa za a gudanar da ayyukan cigaban ‘yan kasa ne. BBC Hausa.

 

 

Mai rahoto;

M.B.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid January 10, 2025 January 10, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Biyan kudaden jarabawar NBAIS – NAPAIS ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano

Attajdid Attajdid November 4, 2025
Ana Cigaba da Kaiwa Juna Hari Tsakanin Isr@’ila da Dakarun Muk’awama a Gaza
Jigawa To Award N1.2 Billion Contract For Solar Powered Street Light
AN FARA CIRE TSAMMANIN MUTANAN DA KUNGIYAR HAMAS TA KAMOSU A HARIN 7 GA WATAN OKTOBA 2024
A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar kano Comrd. Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar kuma aka rabawa manema labarai.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?