By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso 
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso 
News

Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso 

Attajdid
Last updated: 2025/05/18 at 10:09 AM
Attajdid Published May 18, 2025
Share
SHARE

Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso

Jagoran ya ce a yanzu ya zaɓi yin shiru game da abubuwan da ke faruwa a siyasar ƙasar nan.

 

Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ƙaryata wani rahoto da ke yawo cewa yana shirin shiga sabuwar haɗakar siyasa.

 

A wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, Kwankwaso ya bayyana rahoton a matsayin “karya, ba shi da tushe kuma makircin wasu ‘yan siyasa ne.”

Ya gargaɗi jama’a da ka da su yarda da irin waɗannan labarai marasa tushe.

 

“An jawo hankalina kan wani rahoto wanda ke bayyana matsayina a haɗin gwiwar siyasa a Najeriya.

 

“Ina so na fayyace cewa irin waɗannan rahotannin ƙarya ne, ba su da tushe kuma makircin siyasa ne kawai,” in ji Kwankwaso.

 

Tsohon ministan tsaron, ya bayyana cewa ya zaɓi ka da ya riƙa yin magana a fili kan wasu abubuwan da ke faruwa a siyasar ƙasar nan, amma zai yi magana a lokacin da ya dace.

 

“Na daɗe da daina yin sharhi kan abubuwan da ke faruwa a siyasa, kuma zan ci gaba da kaucewa yin haka a halin yanzu,” ya ƙara da cewa.

 

Kwankwaso ya buƙaci ’yan Najeriya da su dinga dogaro da hanyoyin sadarwarsa a hukumance idan suna son sanin matsayinsa ko ra’ayinsa game da wani abu.

 

“Dangane da hakan, ina roƙon jama’a da su riƙa duba ko sauraron saƙonni da ke fitowa daga shafukana da sauran hanyoyin sadarwarta kawai,” in ji shi.

 

Aminiya ta ruwaito cewa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, har yanzu yana ɗaya daga cikin manyan ’yan siyasar da ake sa ido a kansu kan yiwuwar yin haɗaka da wata tafiya ta siyasa.

 

Mai rahoto

Mustapha Garba Usman

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid May 18, 2025 May 18, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
Uncategorized

HUKUMAR TSARO TA KASA TAYI DARAR MIKIYA A OFISHIN NLC.

Attajdid Attajdid August 8, 2024
Nigeria Advocate For Palestine State, Nuclear Disarmament, Global Peace
Ana Tuhumar Ma’aikatan Lafiya 47 a Kotu Kan Mutuwar Jarirai a Turkiyya
‘Yar jarida Walaa Al-Jaabari ta rasa ranta tare da ‘ya’yanta 5.
Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba 
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?