Sanarwar ta ce, jami’an sun yi ikirarin cewa suna neman wasu takardu ne da aka yi amfani da su a zanga-zangar matsin rayuwa.Kungiyar wadda ta ce zuwa yanzu ba ta iya tantance abubuwan da jami’an tsaron suka kwashe ba, ta nemi da a gaggauta janye jami’an daga hedikwatar tata. Kungiyar ta bayyana yau a matsayin wata bakar rana a dumukuradiyyar Najeriya, inda ta ce ko da a lokacin bakin mulkin sojoji ba a taba yi wa hedekwatar ta abin da aka yi mata a wannan lokacin ba na kutse.
Asali: Bbc Hausa




