Qassem Brigades Sun Kai wa Sojojin Yahudawan Sahyoniya Farmaki
A majiyar At-tajdid News ta yankin gabas ta tsakiya ta shedamata cewa Mayakan Kata’ibul Qassam sun bayyana cewa sun samu nasarar tarwatsa wata tankar yaki ta Yahudawan sahyoniya, “Merkavah”, tare da lalata wata babban bulldoze ta sojojin D9. Wannan samame ya faru ne a titi na 8, kudu maso yammacin unguwar Zaytun, a cikin birnin Gaza kamar yadda aka kawo a shafin Kata’ibul Qassem.
Haka zalika, dakarun Qassam sun ce sun tarwatsa wata motar daukar sojojin ‘yan sahyoniya da wani bam da aka dasa shi a cikin karkashin ƙasa, wanda ya haifar da ƙonewar motar gaba ɗaya. Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa an hango jirgin sama mai saukar ungulu na sojojin abokan gaba yana sauka a yankin Nuzla, yammacin Jabaliya, arewacin Gaza, domin ceto sojojin da abin ya rutsa da su.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




