By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Shugaban Gwamnatin Sudan ya ce ba Zai Yiwu RSF ta Koma Matsayinta na Baya ba
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Shugaban Gwamnatin Sudan ya ce ba Zai Yiwu RSF ta Koma Matsayinta na Baya ba
International News

Shugaban Gwamnatin Sudan ya ce ba Zai Yiwu RSF ta Koma Matsayinta na Baya ba

Attajdid
Last updated: 2025/01/02 at 11:24 AM
Attajdid Published January 2, 2025
Share
SHARE

Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Sudan ya ce ba zai yiwu ba rundunar RSF ta koma matsayin da take kafin a fara yaƙi.

 

Abdel Fattah al-Burhan ya yi wannan kalaman ne ranar Talata a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na ƙasar Sudan domin murnar cika shekara 69 da samun ‘yancin kan ƙasar daga Birtaniya.

 

Sai dai kuma ya bayyana cewa zai “shiga duk wani shiri da zai kawo ƙarshen yaƙin tare da tabbatar da dawowar fararen-hula gidanjensu cikin aminci.”

 

“Yanayin ba zai koma yadda yake kafin ranar 15 ga watan Afrilu 2023 ba kuma ba za mu yarda da kasancewar waɗannan masu kisan kai da laifuka da magoya bayansu a cikin al’ummar Sudan ba,” a cewar Burhan a lokacin da yake magana kan RSF.

 

Ya ƙara da cewa mayaƙan RSF suna gana wa mutanen Sudan uƙubar kisa da yunwa da kuma gudun hijira.

 

Yaƙin basasar Sudan

 

Kimanin mutane 25,000 ne aka kashe kuma aka raba miliyan goma da gidajensu tun watan Afrilun shekarar 2023 a lokacin da aka fara yaƙin neman iko tsakanin sojin Sudan ƙarƙashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da rundunar RSF ƙarƙashin mataimakinsa a wancan lokacin, Mohamed Hamdan Dagalo.

 

Yaƙin ya watsu zuwa jihohi 13 cikin 18 na ƙasar Sudan, lamarin da ya janyo bala’in lalata abubuwa da kuma tura miliyoyin mutane cikin yunwa da mutuwa.

 

Jerin ƙoƙarin shiga-tsakani da wasu ƙasashe suka jagoranta ciki har da Amurka da Saudiyya bai yi nasarar tabbatar da tsagaita wuta ba tukunna yayin da ɓangarorin sojin Sudan da RSF ke zargin juna da yi wa yunƙurin sulhu zagon ƙasa. TRT Africa Hausa.

 

 

Mai rahoto;

M.B.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid January 2, 2025 January 2, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Nigeria Advocates Strategic Collaboration To Address Security Challenges In West Africa 

Attajdid Attajdid March 13, 2025
Governor Namadi Promises Timely Completion of N6.4 Billion Naira Basirka Bridge  
Yahudawan Sahyoniyya Sun Kai Jiran Hare-hare Sama da Ashirin (20) a Gaza
Kano Distributes Motorcycles, Vehicles to Support Healthcare Programmes Kano State Governor, Alhaji Abba Yusuf, on Thursday, distributed 88
Ga dukkan alamu za a gwabza yaƙi tsakanin Isra’ila da Iran — Fidan
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?