Dai-dai lokacin da Amurka take k’ok’arin tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran ta tabbata.
A yankin Gaza ana ci gaba da samun kaiwa juna hari tsakanin dakarun muk’awama da Yahudawan s
Sahayoniya.
Kamar yadda majiyar At-tajdid News ta yankin Gabas ta tsakiya ta samu daga hukumar lafiya ta yankin, Isr@’ila ta kai hari ranar laraba da safe a yankin Zirin Gaza da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 51 da kuma samun mutane 14 da suke karbar agaji a wajan ma’aikatan lafiya.
Saraya al-Quds sun kai wa motocin ‘yan kama wuri zauna hari da ya yi sandiyar lalacewar motocina yankin Abasan al-Kabira da ke gabashin Khan Yunus. A wani kwantan b’auna da Al-Qassam Brigades ta kai wa wani jirgin ruwan yahudawan sahayoniya hari, tare da k’ona shi da ma’aikatansa a yankin Khan Yunis.
Mai rahoto,
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




