‘Isra’ila ta amince da shawarar tsagaita wuta a Gaza’
Kafafen yaɗa labarai a Isra’ila sun ce firaminista Benjamin Netanyahu ya amince da tayi na baya-bayan nan kan tsagaita wuta a Gaza wanda Amurka ta gabatar.
Sai dai an ruwaito firaministan na shaida wa iyalan waɗanda ake garkuwa da su a Gaza cewa sojojin ƙasar ba za su bar Gaza ba har sai an ceto dukkanin waɗanda ake tsare da su.
Wakilin BBC ya ce hakan na zuwa ne yayin da alamu ke nuna cewa Hamas na dab da yin watsi da tayin.
Wani babban jami’in Falasɗinawa ya shaida wa wakilin cewa Amurka ta nuna son kai a cikin yarjejeniyar, inda ta bai wa Isra’ila fifiko, musamman game da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta kai ga tsagaita wuta ta kwana 60, yayin da za a saki mutane 10 da ake garkuwa da su.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




