HALIN DA AKA TASHI DA SHI A GAZA
Wakilin gidan talabijin na Aljazeera Ashraf Abu Amra ya ce “harin bama-bamai na mamaya bai tsaya ba kuma ana ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin mamaya da kuma ‘yan adawar a Gaza” (kunyoyin mukawama).Dakarun mamaya sun tarwatsa gidaje a unguwar Sheikh Nasser da ke gabashin Khan Yunis.
Daga majiyoyin lafiya na Al Jazeera:
An kai gawarwakin shahidai 8 zuwa cibiyar Kiwon lafiya ta Nasser da ke garin Khan Yunis tun da safiyar yau.Mamayar ta yi kisan kiyashi na mutane 3 a zirin Gaza, da suka hada da shahidai 39 da jikkata 93 a asibitoci cikin sa’o’i 24.
Ma’aikatar lafiya a Gaza: -Ta ce adadin wadanda suka mutu a harin ta’addancin Isra’ila ya karu zuwa shahidai 39,363, yayin da wasu 90,923 suka jikkata tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.
Mai rahoto;
Musa Badamasi Gama.
At-tajdid News.




