By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Turkiyya da Masar suna da buƙatu iri ɗaya kan lamuran da suka shafi Falasɗinawa, kuma dukkansu suna son ganin Isra’ila ta gaggauta daina kai hare-hare a Gaza, a cewar Shugaba Recep Tayyip Erdogan.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Turkiyya da Masar suna da buƙatu iri ɗaya kan lamuran da suka shafi Falasɗinawa, kuma dukkansu suna son ganin Isra’ila ta gaggauta daina kai hare-hare a Gaza, a cewar Shugaba Recep Tayyip Erdogan.
International News

Turkiyya da Masar suna da buƙatu iri ɗaya kan lamuran da suka shafi Falasɗinawa, kuma dukkansu suna son ganin Isra’ila ta gaggauta daina kai hare-hare a Gaza, a cewar Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Attajdid
Last updated: 2024/09/05 at 7:41 AM
Attajdid Published September 5, 2024
Share
SHARE

“Gudunmawar da Turkiyya da Masar suke bayarwa wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tana da matuƙar muhimmanci,” in ji Erdogan ranar Laraba, a yayin da yake gabatar da jawabi ga manema labarai tare da takwaransa na ƙasar Masar Abdel Fattah el Sisi, wanda ke ziyarar aiki a Turkiyya.

Wannan ce ziyarar aiki ta farko da Sisi ya kai Turkiyya tun da ya soma mulki a 2014. Ya kai ziyarar ce sakamakon gayyatar da Erdogan ya yi masa.

A wani ɓangare na ziyarar da Sisi yake yi, shugabannin biyu sun jagoranci wani Babban Taro Kan Haɗin-Kai tsakanin ƙasashen biyu tare da sanya hannu kan yarjeniyoyi 17 a fannoni daban-daban.

“Mun jaddada aniyarmu ta haɗin-kai a dukkan ɓangarori, ciki har da masana’antu da cinikayya da tsaro da kiwon lafiya da muhalli da makamashi,” a cewar Erdogan, wanda ya ƙara da cewa ƙasashen biyu za su kyautata alaƙa a tsakaninsu ta yadda kowane ɓangare zai “ci moriyarta.”

A nasa ɓangaren, Sisi ya ce ziyarar da ya kai Turkiyya “ta buɗe sabuwar hanya a fannin tattalin arziki da cinikayya,” sannan ya jaddada matsayin ƙasashen biyu game da “wajabcin tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo ƙarshen hare-haren da Isra’ila take kai wa a Gabar Yammacin Kogin Jordan.”

DAɗAɗɗEN TARIHI NA ABBATO
Turkiyya da Masar, waɗanda suka kasance biyu daga cikin manyan ƙasashen Gabas ta Tsakiya, suna ci gaba da ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu a wani ɓangare na shirin ƙara kusantar juna da suka ƙaddamar shekaru uku da suka gabata.

A watan Fabarairu, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai ziyara Masar, inda ya gana da Sisi tare da sanya hannu kan yarjeniyoyi a fannin yawon buɗe ido da al’adu da ilimi.

Cinikayya ita ce maƙasudin ƙarfafa alaƙa a tsakanin Turkiyya da Masar. Ƙasashen biyu suna fatan ƙara cinikayya a tsakaninsu da aƙalla kashi 50, wato daga dala biliyan 10 zuwa dala biliyan 15.

Turkiyya na cikin manyan ƙasashen da suka fi gudanar da harkokin kasuwanci da Masar a shekaru 10 da suka gabata.

Ƙasashen biyu suna da daɗaɗɗen tarihi na abota. A shekara mai zuwa ne Turkiyya da Masar za su cika shekara 100 da ƙulla dangantakar diflomasiyya.

SANARWAR HAɗIN-GWIWA
A sanarwar haɗin-gwiwar da Turkiyya da Masar suka fitar bayan kammala Babban Taro Kan Haɗin-Kai a tsakaninsu, Ankara da Kairo sun jaddada haɗin gwiwarsu wajen goyon bayan Falasɗinu da kawo ƙarshen hare-haren da Isra’ila take kai wa Gaza.

Ƙasashen biyu sun ce Falasɗinawa suna da ‘yancin samun ƙasa mai cin gashin kanta, wadda Gabashin Birnin Ƙudus zai kasance babban birninta, bisa iyakokin da aka shata a 1967. Kazalika sun jaddada matsayarsu ta kare ‘yancin Falasɗinawa da aka kora daga gidajensu.

Haka kuma sun jaddada goyon bayan Iraƙi a matsayin ƙasa mai ‘yancin kansa da ke neman zaman lafiya, tare da goyon bayan ci gaban Iraƙi da yunƙurin sake gina ta.

Kazalika Turkiyya da Masar sun jaddada goyon bayansu ga tsarin siyasar al’ummar Libya kamar yadda MDD take yi, wada zai kasance mataki na tabbatar da zaman lafiya da tsaro da haɗin-kai na Libya.

Da suke bayyana takaicinsu kan yaƙin Sudan, ƙasashen biyu sun koka kan halin rashin jinƙai da take ciki, wanda suka ce zai ƙara ta’azzara yanayin rashin jinƙai a yankin, kana suka yi maraba da yunƙurin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar cikin diflomasiyya.

Mai rahoto;
Mujaheed Tasi’u.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid September 5, 2024 September 5, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Jama’ar gari sun kashe DPO, sun ƙona ofishin ’yan sanda a Kano

Attajdid Attajdid May 28, 2025
Rundunar yan sandan jihar Gombe ta cafke wasu matasa biyu da ake zargi da kashe wani matashi mai suna Dauda Ahmed dan shekara 22 a garin Kumo da ke karamar hukumar Akko a jihar.
Gaza anti-war protesters clash with police at Australian arms fair as police deploy tear gas and stun grenades to disperse crowd flinging horse manure and setting bins alight.
Zulum ya jaddada kudirinsa na sake tsugunar da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa
NG-CARES Distributes Motorcycles to Facilitators in Jigawa
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?