Ana Cigaba Kashe ‘Yan Jaridu a Gaza Sakamakon Harin Yahudawan Sahyoniya a Gaza
Aljazeera Mubasher ta ruwaito cewa an samu gagarumin asarar rayuka sakamakon sabon hari da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza.
Rahotanni daga wurin sun tabbatar da cewa mutane 9 sun mutu bayan da wani gini a Cibiyar Lafiya ta Nasser a Khan Younis ya gamu da ruwan bama-baman Isra’ila. Daga cikin wadanda suka mutu akwai ’yan jarida biyu, Hossam al-Masri da Mohammed Salama.
Bayan wannan hari, Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa hari na biyu ya sake aukuwa lokacin da jami’an gaggawa suka isa wajen domin ceto wadanda suka jikkata da kuma jikkunan wadanda suka mutu.
Daga baya, rahotanni sun tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu ya haura zuwa 14, ciki har da ’yan jarida uku ciki har da maca ‘yar jarida Maryam Abu Daqah, da mai daukan hoton Aljazeera Mohammed Salama, da kuma Hossam al-Masri.
Harin ya afka kai tsaye kan ginin karɓar marasa lafiya da sashen gaggawa a cikin asibitin Nasser, lamarin da ya jefa dubban mutane cikin firgici da rudani.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




