Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars ta ‘yan ƙasa da shekara 19, da ke Nijeriya, (Kano Pillars FC U-19) ta yi hatsarin mota a kan hanyar zuwa Jos don yi wani wasa da ƙungiyar Plateau United U-19, kamar yadda mai magana da yawun ƙugniyar, Abubakar Isa Dandago ya fada a shafinsa na Facebook a ranar Talata.
Ba a samu asarar rayuka ba amma ‘yan wasa da dama da direban motar sun ji raunuka kuma tuni aka garzaya da su asibiti don ba su kulawa.
At-tajdid News




