A ranar Talata ne aka wayi gari gidajen mai mallakar kamfanin na NNPCL sun ƙara farashin da ake sayar da man fetur ɗin.
Kafinnan Babban kamfanin Mai Na kasar NNPCL a ranar lahadi ta gabata 1 ga wata September 2024 ya bayyana irin mummunar matsalar da yake fuskanta ta bashi wadda ke ganin hakan barazanace da zata iya gurgunta tsarin kamfanin na shigo da tataccen Mai daga kasashen waje.
Kamar yadda mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye ya fitar ranar Lahadi, ya ce “ɗimbin bashin ya sanya matsi sosai kan kamfanin kuma yana barazana ga ɗorewar shigo da fetur”.
Sai gashi katsam an tashi da sabon farashin man fetur kamar yadda bayanai daga sassan Nijeriya daban-daban na cewa sabon farashin ya bambanta, inda ake sayar da lita daya a Legas a kan naira 855 yayin da a wani bangare na shiyyar arewa maso yamma kuma ake sayar da shi a kan naira 904.
A can bangaren arewa maso gabas kuma farashin fetur din ya kai naira 924 a kan kowace lita daya.
At-tajdid News.




