By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: An Baiwa Babban Jami’in Binance Gambaryan Izinin Barin Nijeriya Bayan Janye Tuhumar da Ake Masa
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > An Baiwa Babban Jami’in Binance Gambaryan Izinin Barin Nijeriya Bayan Janye Tuhumar da Ake Masa
News

An Baiwa Babban Jami’in Binance Gambaryan Izinin Barin Nijeriya Bayan Janye Tuhumar da Ake Masa

Attajdid
Last updated: 2024/10/25 at 3:19 AM
Attajdid Published October 25, 2024
Share
SHARE

Gwamnatin Nijeriya ta janye ƙarar da ta shigar ta shugaban kamfanin Binance Tigran Gambaryan kan zargin halatta kudaden haram, domin ba shi damar zuwa asibiti a kasar waje, kamar yadda lauyan gwamnatin ya bayyana a ranar Laraba.

 

Gambaryan, wanda Ba’amurke ne, kuma shugaban kamfanin hada-hadar kuɗaɗe na Binance, yana tsare a Nijeriya tun daga karshen watan Fabrairu kuma ana tuhumarsa da karkatar da sama da dala miliyan 35.

 

Gambaryan da Binance sun musanta zargin.

 

Amma za a ci gaba da shari”a a kan zarge-zargen ƙin biyan haraji ta daban da ake yi wa kamfanin Binance, mafi girman kamfanin musayar crypto na duniya. Binance ya kuma musanta wadannan tuhume-tuhumen.

 

Wannan mataki ya biyo bayan bayanan da wani jami’in hukumar gidajen yarin Nijeriya NCoS ya bayar ne, wanda ya bayyana a gaban kotun a ranar ƙarshe da aka saurari ƙarar, wadda Gambaryan bai samu zuwa ba saboda rashin lafiyarsa.

 

Daga nan ne aka sake ɗage zaman shari’ar zuwa yau talata saboda muhimmancin gaggauta shari’ar.

 

A yayin da aka koma sauraron ƙarar, lauyar EFCC R. U. Adagba ta shaida wa Mai Shari’a Nwite matakin gwamnatin tarayya na janye ƙarar da ake yi wa jami’in Binance din saboda taɓarbarewar lafiyarsa.

 

Ta ce bayanan da suka samu kwanan nan daga jam’in hukumar gidajen yarin ta hannun ofishin Babban Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro ya nuna cewa jikin Gambaryan ya tsananta sosai ta yadda ko tafiya ba ya iya yi sai a kan keken marasa lafiya.

 

Adagba ta kuma ce baya ga rashin lafiya, Gambaryan na buƙatar a yi masa tiyata wadda kuma zai ɗauki lokaci yana jinya.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid October 25, 2024 October 25, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Biyan kudaden jarabawar NBAIS – NAPAIS ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano

Attajdid Attajdid November 4, 2025
PDP Has Never Won a Gubernatorial Election in Jigawa — Hon. Galambi
YAN BINDIGA SUN KASHE HADIMIN GWAMNA DA MATARSA, ‘YAN SANDA SUN MAGANTU
Jigawa APC Vows Not Condoned Attack On Defense Minister Other Party Leaders
Yin sulhu da ’yan bindiga dabara ce ba gazawa ba — Gwamnatin Sakkwato
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?