Biyan kudaden jarabawar NBAIS – NAPAIS ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano
Kungiyar National Association of Proprietors of Arabic and Islamiyya Schools (NAPAIS) ta yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa ci gaba da goyon bayansa da jajircewarsa wajen bunkasa ilimin addinin Musulunci a cikin jihar.
Yabon ya fito ne daga Shugaban Kungiyar na Arewa maso Yamma (North West Zonal Chairman), Malam Aliyu Ibrahim Sani Mainagge, a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamba, 2025.
A cewar Malam Mainagge, “Lallai ya kamata mu yaba wa Gwamnan Jihar Kano bisa irin kokarinsa da rashin gajiyawa wajen ganin cewa daliban da ke karatun Arabiyya da Addinin Musulunci suna da damar ci gaba da karatu cikin inganci.”
A zaman Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025, majalisar ta amince da biyan kudi har ₦308,957,001.00 (Naira Miliyan Dari Uku da Takwas, Dubu Dari Tara da Hamsin da Daya) ga Hukumar Shirya Jarrabawar Arabiyya da Addinin Musulunci ta Ƙasa (NBAIS) domin a fitar da sakamakon jarrabawar daliban makarantun Arabiyya da Islamiyya, don ba su damar ci gaba da karatunsu na gaba da sakandare.
Malam Mainagge ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta ci gaba da irin wannan kokari mai albarka, yana jaddada cewa irin wannan mataki yana da muhimmanci wajen gina al’umma mai nagarta da ilimi.
Kungiyar National Association of Proprietors of Arabic and Islamiyya Schools (NAPAIS) ita ce ƙungiyar dake haɗa masu makarantun Arabiyya, Islamiyya da Tsangayu a duk faɗin Najeriya, domin ci gaban ilimin Musulunci da kyautata tarbiyyar al’umma.
Sa hannu:
Malam Aliyu Ibrahim Sani Mainagge
Shugaban Arewa Maso Islamiyya Schools (NAPAIS)
At-tajdid News.




