By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Yahudawan Sahyoniyya Sun Kai Jiran Hare-hare Sama da Ashirin (20) a Gaza
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Yahudawan Sahyoniyya Sun Kai Jiran Hare-hare Sama da Ashirin (20) a Gaza
News

Yahudawan Sahyoniyya Sun Kai Jiran Hare-hare Sama da Ashirin (20) a Gaza

Attajdid
Last updated: 2025/10/20 at 7:31 AM
Attajdid Published October 20, 2025
Share
SHARE

Yahudawan Sahyoniyya Sun Kai Jiran Hare-hare Sama da Ashirin (20) a Gaza

 

 

Rahotanni daga yankin Gaza sun tabbatarwa  da At-tajdid  News cewa an samu mutane da dama da suka rasa rayukansu da wasu da suka jikkata bayan harin da jiragen yaki na Isra’ila suka kai kan wani café mai suna “Twix”, da ke yammacin az-Zawaida, da ke tsakiyar Gaza.

 

Hukumomi a asibitin Shahidan Al-Aqsa sun tabbatar da karɓar gawarwaki da raunana masu yawa sakamakon harin da aka kai a rana ta yau.

 

A wani rahoto, tashar i24 ta rawaito daga wani jami’in tsaro na Isra’ila cewa sojojin saman Isra’ila sun kai hare-hare sama da ashirin (20) a cikin Gaza tun daga safiyar yau, suna mai cewa hare-haren na nufin tunkarar barazanar makamai daga ƙungiyoyin ’yan gwagwarmaya.

 

Daga cikin hare-haren, rahotanni sun tabbatar da shahadar mutum goma sha ɗaya (11) tare da raunuka da dama, a yankunan az-Zawaida, an-Nuseirat, da Jabalia.

 

A sansanin Al-Bureij, jiragen Isra’ila sun kai hari kan gidan iyalin Abdulhadi, inda aka samu hasarar rayuka da lalacewar dukiya.

 

A yankin ash-Shalayhat, kudu maso yammacin az-Zawaida, wani hari ya hallaka mutane da dama bayan bam ya fada kan wata tantar jama’a, inda mutane ke neman mafaka daga hare-haren baya-bayan nan.

 

A gefe guda, Kata’ib al-Qassam, ɓangaren soji na Hamas, ta fitar da sanarwa tana cewa:

 

“Muna nan kan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma, kuma ba mu da wata alaka da abin da ke faruwa a yankin Rafah.”

 

Ƙungiyar ta bayyana cewa yankin Rafah yana karkashin ikon mamayar Isra’ila, kuma sadarwa da mayakanta da ke can ta katse tun watan Maris, lokacin da yaƙi ya sake ɓarke wa.

Ta ce ba ta da tabbacin ko mayakanta suna raye ko a’a.

 

A yankin Khan Younis kuma, jirgi maras matuki na Isra’ila ya kai hari a yankin Al-Mawasi, wanda ya janyo tsoro da fargaba a cikin jama’a.

Masu aikin gaggawa na ci gaba da neman mutanen da suka ɓace a yankunan da aka kai hari.

 

Wasu jami’an Amurka sun shaida wa kafafen yada labarai cewa gwamnatin Amurka ba za ta bari rikicin Gaza ya koma cikakken yaƙi ba, duk da cewa lamarin na ƙara yin muni a kowace rana.

 

Masu lura da al’amuran yankin na gargadi cewa yanayin jin kai a Gaza na kara tabarbarewa, yayin da asibitai suka cika, kuma kayan agaji su ke ƙarewa.

 

Mai rahoto;

M.B.S.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid October 20, 2025 October 20, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Dakarun Isra’ila Sun Kai Hari a Sansanin ‘Yan Gudun Hijira Mawasi Khan Yunis

Attajdid Attajdid September 10, 2024
Labarai Cikin Hotuna
Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Halarci Bikin Naɗin Paparoma Leo XIV a Vatican
Masu Karbar Kayan Agaji a Gaza Suna Fuskantar Baraza
Effective Family Planing: Key to Sustainable Safe Motherhood  
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?