Harkar Hamas: Wani sabon mummunan kisan kiyashi da sojojin yahudawan sahyuniya suka yi a garin Mawasi Khan Yunis ta hanyar kai wa tantunan ‘yan gudun hijira hari da makamai masu linzami.
Kisan da sojojin mamaya suka yi a Khan Yunis ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama, mafi yawansu mata da kananan yara sabanin yadda a yau ne daliban makaratun Isra’ila suke komawa makarantun su cikin walwala.
Ikirarin da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi na cewa akwai ‘yan gwagwarmaya a wurin da aka kai hari, bahabane dakarun mukawama sun tabbatar da kin kasancewar wani daga cikin mambobinta a cikin tarukan farar hula ko kuma amfani da wadannan wuraren don dalilai na tsaro.
At-tajdid News.




